Polaroid
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Tambayoyi da amsarsu tare da Mallam Ibrahim Zakzaky na goma

Sayyed Zakzaky2

Ko ya halasta mutum ya yi wa 'yarsa auren dole?

TAMBAYA: Akramakallah. Ko mace za ta iya zuwa makarantar da gwamnati ta bude don koya wa mata sana'a?

Daga Jamila Ya'u Kabuwa, Abuja

SHAIKH ZAKZAKY: Abin da ya kamata ya zama shi ne kawai, mace za ta iya zuwa makaranta don koyon sana'a? Da alama abin da ya dami ita mai tambayar ita ce gwamnati ce ta bude. To, in dai ba wadansu ka'idodi ne aka gindaya wadanda suke saba wa shari'a ba, shi kenan sunanta makaranta kawai.


TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam. Wadanne hanyoyi ya kamata mutum ya bi kafin ya saki matarsa?

Daga Salisu Jibirnin Sammawa Kano

SHAIKH ZAKZAKY: Matakai ne kamar hudu ko biyar. Na karshensu ne saki. Amma a takaice akwai wa'azi; akwai kaurace mata; akwai ya dan yi mata fada; da zare ido, idan duk wannan bai yi ba. Ya danganta da abin da ya sa yake so ya sake ta din ne. Sannan kuma in hakan ya ki sai a nemo masu sasantawa - da nasa bangaren da nata bangaren. Sai in ya ki, ya zama dai kawai maslahar shi ne saki, to shi ne sai ya jira har sai ta yi tsarki daga haila, kuma a lokacin tsarkin bai tabe ta ba. Sannan ya yi 'insha'in' saki din ga shaidu, adalai guda biyu akalla.

TAMBAYA: Akramakallh. Zai kira shaidun ne ya ce ku shaida na saki matata, ko sakinta kawai zai yi?

Daga Salisu Jibrin Sammawa Kano

SHAIKH ZAKZAKY: A'a ba lalle ne ya ce masu su yi shaida ba. Idan dai a gaban adilai ya yi, ko bai ce masu ku zo ku yi shaida ba, sun zama shaidu. Abin nufi dai a yayin da ya yi 'inshain' sakin, wasu mutane adilai sun ji. Amma ba lalle ne ya ce wane da wane ku zo ku yi mani shaida ba.

TAMBAYA: Ko ya halatsa mutum ya yi wa 'yarsa auren dole?

Daga Salisu Jibrin Sammawa Kano

SHAIKH ZAKZAKY: Idan yarinya ce karama wacce ba ta balaga ba, ba ta hankalta ta san wanene ya kamata ta aura ba, kuma maslaha ne aurar da ita, saboda wani dalili masalan, kamar lafiyarta ko wani abu, ko don jin tsoron lalacewarta, ko abin da ya yi kama da haka nan, kuma ya sami wanda ga nazarin shari'a, shi ne ya fi dacewa. amma sai ya zama ita saboda rashin hankali, tana ganin ba shi ne ya fi ba, to a nan ne kawai yake da iko. To, amma kuma Uba ne kawai da Kaka, wato Uban Uba suke da wannan. Amma in banda haka, shi aure ana so ya kasance akwai neman yardar yarinya. Har ma aka ce wacce ta taba aure, wato bazawara kenan, ta amsa da bakinta ta ce "eh." Karamar yarinya kuma ta ba da izini da yin shiru. Wannan ana son haka nan, sai dai idan maslaha ne ya zama dole. Sai in dole ne za a cimma wannan maslala din, to wannan kuwa.

TAMBAYA: Akramakallah. Ko halasta mutum ya rika amfani da kayan da ya jingina, kamar gona, gida, ko mota?

Daga Salisu Jibrin Sammawa Kano

SHAIKH ZAKZAKY: To da ma jingina, kamar yadda sunan ya nuna da Hausa, ana jingine abin ne, har sai ya biya bashin sai ya zo ya karbi kayansa. Saboda haka ba a amfani da kayan jingina. Wannan shi ne abin da aka sani cewa; mutum in ya karbi ko da gona ce, ba zai noma ta ba. Za a bar ta ne har sai ya biya bashin, sannan sai ya mai da wa mai kayan. Sai dai idan da ma tun farko a yarjejeniyar ya ce, "to idan ruwan shuka ya fadi fa, na samu in noma gonar nan?" Domin gonar tana nan a gonar mai gona. "Kuma in na noma nawa zan ba ka? Tunda gonar tana nan a gonar mai gona, ba ta zama gonar wanda ya karbi jingina ba. Saboda haka sai zama ya ba shi izini in har bai iya biyan bashin ba shi ya noma gonar, amma ya ba shi galla. Ko kuma ya zauni gidan (in gida ne) ya biya shi haya. Ko in wani abin amfani ne ya yi amfani da shi, amma ya biya shi haya. In ya yarda, in an yi yarjejeniyar a kan haka. In ba haka ba ajiyewa ake yi har sai ya biya bashi din.

TAMBAYA: Akramakallah. Mutum ne ya gina masallaci a gidansa, daga baya sai matsalar kudi ta same shi. Ko zai iya matsar da masallacin ya yi amfani da filin?

Daga Salisu Jibrin Sammawa Kano

SHAIKH ZAKZAKY: To masallatai dai iri-iri ne dama, akwai masallacin gida, wanda yake mutum ne ya kebance wani wuri a cikin gidansa don ya rika salla, ko ma a dakinsa ne ma. Daidai inda ka yi shimfida kake salla a dakinka ana ce masa masallacinka, in ka so kana iya canza wannan, irin na gida. Akwai masallacin Unguwa, akwai wanda ake ce ma masallacin kabila, ko masallacin gari, na Juma'a kenan. To su na kabila da na gari, wannan har abada na Allah ne. Saboda haka ba za a je gare su da wani abu ba sai abin da zama maslaha. Yana iya halatta idan ya zama maslaha ne ga masallacin da al'ummar da suke salla su canza wa masallacin wuri. Wannan zai yiwu. Ko kuma wani dalili wanda yake don maslahar al'umma, ko hanya, ko hanyar ruwa, ko wani abu da ya yi kama da haka nan, ya tilasta a yi haka nan, ana iya yi. Saboda haka in masallacin gida ne yake nufi, wannan duk abin da ya ga dama yana iya yi. Amma in masallacin Unguwa ne, to, da ma na al'umma ne, ba nasa bane.

TAMBAYA: Akwai kuma wadanda masu kudi kan gina a gidajensu wanda ake ce wa "Allah-ga-naka"?

MALAM ZAKZAKY: To idan masallacin gida, duk yadda ya ga dama yana iya yi da shi saboda shi masallacin gida bai da wannan matsayin masallacin Unguwa da na Juma'a.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, shin me ke kawo girgizar kasa ne, fushin Allah ne ko yanayi ne?

Daga Magaji Mai Wada Kazaure

MALAM ZAKZAKY: To ita girgizar kasa tana daga cikin ayoyi. Don haka ne ma ake yin sallar Aya a lokacin da ta auku, kamar na khusufin wata da rana, duk ana yin sallolin ayoyi. Ko ma wadansu abubuwa wadanda mutane sukan gani, wadanda ba a saba ba, masu figitarwa. Amma ita girgizar kasa tana iya zuwa ta hanyoyi daban-daban. Kamar yadda ka san yawan ruwa, ko ambaliyar ruwa shi ma yana iya zuwa. Amma ba yadda za a yi mutum ya ce lalle in ya auku yana nufin fushin Allah ne. Kodayake Allah (T) ya halaka wasu al'ummu a baya da girgizar kasa. Amma ba wai lalle abin da yake nufi kenan ba, domin yanayi na iya kawo shi, tunda in ka lura a wadansu wurare ba ma a yin ta sam, kamar mu a nan nahiyarmu ba a san ta ba. Ga wadansu wurare, kuma wuri ne mai yawan aukuwa kowane lokaci. Domin ana cewa a cikin motsin duwatsu da ke karkashin kasa ne ke kawo ta, wanda wani dutsen nan da nan sai ya motsa ya je wani wuri, sai ya bar wagegen gibi na kasa, sai ya rinka tasowa sama, har yayin da ya bayyana sama sai kasa din ta yi motsi. To kuma wannan akwai wuraren da ake yawan samun sa.

TAMBAYA: Shin mutum zai iya yin hijira zuwa wata kasar da ake yin shari'a Musulunci, musamman a irin wannan lokacin?

Daga Magaji Mai Wada Kazaure

SHAIKH ZAKZAKY: Ina ganin ita hijira ai ba wai kawai haka nan kawai kana zaune ne sai ka ce bari ke tashi ka yi hijira ba. Da haka Annabi (S) ya yi da ba a sami addini ba. Zai gudu kenan. Ba sai ya tashi ya yi kira ga shari'a din ba? Ai sai ya yi ta kokari a yi shari'a din. Amma na'am, idan ya ga akwai wani muhalli da ake addini wand yake can ya fiye masa, in ya fita can ba laifi. Sai dai ba sunansa ya yi hijira bane, sunansa ya gudu ne!

TAMBAYA: Dangane da yadda mutanen gari suke sakin matansu shin sun saku, kuma dan uwa na iya aura?

Daga Magaji Mai Wada Kazaure

SHAIKH ZAKZAKY: To idan ya inganta a wajen su mutanen garin shi kenan, ko da a wurinsa shi bai inganta ba, in dai a wurinsu bisa mazhabarsu a yadda suke gani a hukuncin da ke hannunsu cewa wannan matar ta saku, to shi kenan ta saku din. Shi ma sai ya iya auren ta. Kamar alal misali wadda ta gama idda bayan an sake ta saki uku a kalma daya masalan, mu a wurinmu wannan sakin bai inganta ba, ba ta 'ba'intu' daga gare shi ba, amma tunda su suna ganin ta 'ba'intu' shi kenan. Ba zai ce tunda an yi sakin da ya saba ka'ida a wurina, saboda haka ta nan a matar wancan mutumin ba, don shi mutumin a ganinsa an riga an gama, ita ma tana ganin an riga an gama. Saboda haka ita ba matar wancan bace, in ta gama iddarta shi kenan za ta iya halatta gare shi ya aure ta.

.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din